Kungiyar ECOWAS za ta Kafa Dakarun ko-ta-Kwana Don Yaƙi da ‘Yan Ta’adda
Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka Ecowas ta ce za ta kafa dakarun ko-ta-kwana domin tunkarar matsalar ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi da ke tayar da zaune tsaye a ƙasashe daban-daban, kamar yadda shafin intanet na The Nation mai zaman kansa a Najeriya ya rawaito.
Read Also:
Kwamishinan Ecowas Abdel-Fatau Musah ya fadi hakan ne jiya a Abuja cewa ƙungiyar na bukatar tara dala biliyan 2.4 ga dakarun, inda ƙasashe mambobin kungiyar suka bayar da rabin adadin.
“A yau, Burkina Faso ta zarce Afganistan a matsayin kasa mafi fama da ta’addanci a duniya kuma Afirka ta zama gida ga kungiyoyin ta’addanci,” in ji Musah.
Shugabannin sojojin Mali da Burkina Faso da Nijar dai sun janye daga kungiyar ta Ecowas a farkon wannan shekarar, bayan da suka zarge ta da rashin tallafa musu wajen tunkarar tashe-tashen hankula daga kungiyoyin al-Qaeda da IS a tsawon shekaru.