Badakalar N5.78bn: EFCC ta Sake Gurfanar da Tsohon Gwamana, Abdulfattah a Gaban Kotu

 

Jihar Kwara – Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta sake shigar da wasu sababbin tuhume-tuhume guda 14 kan zargin almundahanar N5.78bn a kan tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfattah Ahmed.

EFCC ta shigar da tuhume-tuhume a kan Abdulfatah da kwamishinansa na kuɗi, Mista Ademola Banu, a gaban wata babbar kotun jihar Kwara ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Mahmud Abdulgafar.

Ana tuhumar mutanen biyu ne saboda zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a waɗanda aka ware da nufin gudanar da wasu ayyuka da kuma tsaron jihar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Meyasa EFCC ta sake gurfanar da mutanen?

Sake gurfanar da tsohon gwamnan da kwamishinan kuɗin ya biyo bayan janye ƙarar ne a makon jiya daga babbar kotun tarayya da ke Ilorin.

An janye ƙarar ne bayan an sauya alƙalin da ke sauraron shari’ar a babbar kotun tarayya da ke Ilorin, mai shari’a Evelyn Anyadike zuwa wata kotu.

Tun da farko EFCC ta fara gurfanar da Abdulfatah da Banu ne a kan tuhume-tuhume 12 na karkatar da kuɗaɗen jama’a a gaban mai shari’a Anyadike a ranar 29 ga Afrilu, 2024, inda suka ƙi amsa laifin da ake tuhumarsu da shi.

Sai dai kuma an sauya alkalin da ke jagorantar shari’ar wanda hakan ya sanya aka faro ta tun daga farko.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here