Hukumar EFCC ta Fara Gudanar da Bincike Kan Dandalin CBEX
A yayin da wasu ƴan Najeriya ke ci gaba da ƙorafe-ƙorafe kan asarar da suka tafka a dandalin saka hannun jari na CryptoBank Exchange (CBEX), hukumar yaƙi da cin hanci EFCC ta sanar da fara gudanar da bincike kan lamarin.
Rahotanni sun ce kuɗin da ‘yan Najeriya suka yi asara a dandalin na CBEX sun kai sama da naira tiriliyan ɗaya.
Read Also:
Hukumar ta shaida wa BBC cewa ta haɗa hannu da rundunar ƴansanda ta ƙasa da ƙasa INTERPOL da hukumar FBI ta Amurka domin yunƙurin gano waɗanda ke da hannu a dandalin na CBEX tare da ganin yiwuwar karɓo wasu kuɗaɗen da suka maƙale.
Hakan na zuwa ne bayan ƙorafin da waɗanda suka sanya hannun jari a dandalin suka yi na cewar sun kasa cire kuɗaɗen da suka sanya.
Mutane da dama sun tafka mummunar asara bayan sun zuba maƙudan kuɗi a dandalin, sakamakon alƙawarin da aka yi musu cewa za su samu ribar kashi 100 bisa 100 na kuɗaɗen da suka sanya cikin wata guda.