Hukumar EFCC ta Gurfanar da Tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah Kan Ta’ammali da Dukiyar Gwamnati
EFCC ta gurfanar da Stella Oduah, tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, bisa zarginta da satar kudade.
Ana zargin ta da wawurar kudade lokacin tana minista, yanzu haka Uduah sanata ce mai wakiltar mazabar Anambra ta arewa.
EFCC tana zargin Oduah da wawura tare da rub da ciki a kan dukiyar gwamnati lokacin tana minista EFCC ta gurfanar da Stella Oduah, tsohuwar ministan sufurin jiragen sama bisa zargin wawurar kudaden al’umma.
An daga zaman da za a yi da ita ranar Talata saboda tsohuwar ministan bata nan.
Read Also:
Yanzu haka Oduah sanata ce mai wakiltar mazabar Anambra ta arewa, kuma ana zargin ta da wasu mutane 8 a wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CR/316/20.
Hukumar tana zargin Oduah da kwasar kudin gwamnati lokacin tana minista, The Cable ta wallafa.
A ranar Talata lauyan EFCC, Hassan Liman, ya sanar da kotu cewa tsohuwar ministan bata riga ta shirya zuwa kotun ba, don haka ya bukaci alkali ya dage karar.
Kamar yadda yace, “Mai girma mai shari’a, yau ne aka gabatar da karar kuma na sanar da hukumar amma ba a riga an sanar da wacce ake kara (Oduah) ba.
“Sakamakon haka ne muke bukatar a dan daga shari’ar.”
Iyang Ekwo, alkali mai shari’a yace aikin masu kara ne su gabatar da wanda suke kara gaban kotu. Don haka ya dage karar zuwa 22 ga watan Fabrairu.