Aikata Zamba: EFCC ta kai Kakakin Majalisar Jihar Ondo Kotu
Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Ta’annati EFCC ta gurfanar da kakakin majalisar jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya, Rt. Hon. Bamidele Oloyeloogun a gaban babbar kotun jiha da ke Akure.
Ana zargin ɗan majalisar tare da wasu mutum biyu da zambar ƙuɗaɗe, zargin da duka mutanen suka musanta.
Lauyan hukumar EFCC Kingsley Kudus, ya nemi kotun da ta ajiye mutanen uku a gidan gyaran hali na Akure yayin da ake ci gaba da shari’ar.
Read Also:
Ya ce duk da cewa mutanen sun musanta zargin da ake yi musu, har yanzu suna ƙarƙashin kulawar kotu yayin da ake ci gaba da shari’ar.
Lauyan waɗanda ake zargin Barrister Femi Emodamori ya shaida wa kotun cewa a shirye yake domin fara shari’ar gadan-gadan.
Ya kuma nemi kotun da ta yi watsi da buƙatar ajiye waɗanda yake karewar a gidan gyaran hali, kamar yadda lauyan EFCCn ya buƙata, yana mai cewa takardar nemin belin da suke cike tana kan ƙa’ida.
Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin mutanen da yake karewa na fama da rashin lafiyar da ke buƙatar kulawar gaggawa.
Daga ƙarshe dai alƙalin kotun mai shari’a Adegboyega Adebusoye ya bayar da belin mutunen tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Mayu mai zuwa.