Hukumar EFCC ta Kama Ma’aikatan Banki 12 da Zargin Satar kuɗaɗe

 

Hukumar yaƙi da almundahana a Najeriya ta EFCC ta kama ma’aikatan banki 12 da zargin satar kuɗaɗe a wuraren aikinsu a Jihar Enugu da ke kudancin ƙasar.

A cewar hukumar, binciken farko-farko da ta gudanar ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun saci kuɗaɗe daga wasu asusu da ba sa aiki a wani daga cikin reshen bankunan da a yanzu ba sa aiki a jihar ta Enugu.

“An tura kuɗaɗen daga asusan da ke rufe zuwa ga mutane daban-daban, kuma tuni EFCC ta gano wanda ya fi kowa samun rabo mai tsoka,” a cewar sanarwar da hukumar ta fitar ranar Asabar.

Mutanen waɗanda suka ƙunshi mata huɗu da maza takwas, an kama su ne a ranar Juma’a kuma za su gurfana a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

An bayyana sunayensu da: Odeniyi Anthony, Deki Kingsley Onyekachi, Oguchukwu Ene, Elendu Chizaram, Anyakora Uchenna, Onah Kingsley, Akwe Elizabeth and Chinenye Grace Acibe, Victoria Ezedie, Chidi-Ukah Obinna, Etoh Lawrence Uzochukwu, Udeze Harrison.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here