Hukumar EFCC ta Kama Mutane 2 Kan Asirin Samun Arziki a Jahar Borno

 

Jami’an hukumar EFCC sun kama wasu mutane biyu kan batun yin asirin samun dukiya a Borno.

Wani Abubakar Bakura ya ce wani Malam Ayu Sugum ne ya ce ya kawo N2.9 ya yi masa asirin yin arziki cikin sati biyu.

Malam Ayu ya amsa cewa ya karbi kudi daga hannun Abubakar sannan ya bashi wani kyalle da magani na ruwa.

Maiduguri, Jahar Borno – Jami’an hukumar yaki da rashawa na EFCC a Maiduguri jahar Borno sun kama mutane biyu kan zargin ‘asirin samun kudi’ a jahar Borno, The Cable ta rawaito.

A cewar EFCC, daya daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Malam Ayu Sugum, ya umurci wani Abubakar Bakura ya sato N2.9m daga wurin wanda ya ke yi wa aiki.

Sugum, da aka gano cewa yana ikirarin cewa yana aiki da iskokai, ya yi wa Bakura alkawarin cewa zai yi masa asiri ta yadda zai zama attajiri cikin kwanaki 14, rahoton The Cable.

Sanarwar ta EFCC ta fitar ya ce:

“Jami’an EFCC na Maiduguri sun kama wani mai ikirarin ‘boka’ ne, Mallam Ayu Sugum, kan zuga wani Abubakar Mustapha ya sato N2.9m (Naira Miliyan 2.9) daga wurin aikinsa da sunan za a masa asirin da zai zama attajiri.”

“An kama shi ne a wani gida da ke Pompomari Bypass, Maiduguri, Jahar Borno bayan an ambaci sunansa yayin bincike kan korafin da wanda Bakura ke yi wa aiki ya shigar.”

Abubakar ya amsa cewa ya sace N2.9m daga wurin mai gidansa ya bawa Ayu

“Bayan kama shi a ranar 8 ga watan Yulin 2021, Bakura ya amsa cewa ya saci kudin mai gidansa. Ya kara da cewa Ayu Sugum ya amshe kudaden daga hannunsa, ya masa alkawarin zai azurta shi cikin makonni biyu.

“Abubakar ya yi ikirarin an bashi wani ruwan magani da kyalle kuma duk lokacin da ya sha maganin ya kan gusar masa da hankali ya manta abubuwa da suka faru tsawon kwanaki kuma daga bisani ya sato kudin ya bawa ‘bokan’.”

Abinda Malam Ayu ya ce?

“Da aka masa tambayoyi, Sugum ya amsa cewa ya bawa Abubakar kyalle da wani ruwan magani ya sha, amma ya yi ikirarin kudin da ya karba hannunsa bai kai N2.9m ba.”

EFCC ta kara da cewa za a gurfanar da mutanen biyu a kotu idan an kammala bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here