Hukumar EFFC ta kama ɗaliban Jami’a 30 da Zargin Zamba a Jahar Kwara

 

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC shiyyar jahar Kwara, ta ce ta cafke wasu dalibai 30 saboda zargin damfara ta intanet a jami’ar jahar Kwara,

Mai magana da yawun EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa an kama wadanda ake zargin ne bayan wani rahoton sirri kan zarginsu da hannu a zamba ta yanar gizo.

Ya ce bayan samun bayanan abun da suke aikatawa ne jami’an hukumar suka dira a wasu dakunan kwanan dalibai tare da yin bincike, lokacin ne aka kama wadanda ake zargin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here