Bitcoin: Hukumar EFCC ta Kama Masu Ta’ammali da Haramtattun Kudin Yanar Gizo

 

Hukumar EFCC ta kame wasu da take zargin masu aikata laifuka ne ta kafar yanar gizo.

Hukumar ta kame wani dan kasuwa mai ta’ammuli da haramtattun kudin intanet, Bitcoin.

Hukumar ta shaida cewa, za ta gurfanar dasu a kotu idan ta kammala binciken da ya dace.

Ofishin shiyyar Ibadan na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Zagon Kasa (EFCC) ya kama wani dan kasuwar bitcoin da laifin aikata zamba a yanar gizo, Premium Times ta ruwaito.

Wanda ake zargin, Ayomide Adebowale, an kama shi a ranar Juma’a, tare da wasu mutum hudu daga wasu wurare biyu a yankin Elebu da ke Ibadan ta Jahar Oyo.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana sauran da aka kama da suna Philip Gabriel, Mayowa Jolaoso Segun, Babatunde Segun Adeyinka da Abiodun Tolulope Emmanuel.

Ya fada cikin wata sanarwa cewa shekarunsu sun kai tsakanin 21 zuwa 37.

“An kama su ne a bayan samun bayanan sirri da Hukumar ta samu kan zarginsu da aikata laifuka masu nasaba da yanar gizo.

“Abubuwan da aka kwato daga wurinsu sun hada da motoci biyu, kwamfyutocin tafi-da-gidanka, wayoyi da wasu takardu da ake zargin suna dauke da bayanan bogi.

“Za a gurfanar da su zuwa kotu da zarar an kammala bincike,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here