Hukumar EFCC ta Kama Tsohon Gwamnan Jahar Imo, Sanata Rochas Okorocha
Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jahar Imo, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Jami’an hukumar sun damke Okorocha ne a yammacin ranar Talata a garin Abuja bayan ya ki amsa gayyatar da suka dinga aiko masa da ita.
An gano cewa a halin yanzu yana hedkwatar hukumar inda yake amsa tambayoyi akan almundahanar wasu tarin kudade Tsohon gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, jaridar Premium Times ta tabbatar.
Jami’an hukumar EFCC sun kama Okorocha wurin karfe 4 na yammacin Talata a ofishinsa dake Abuja, majiya ta tabbatar.
Read Also:
Majiyar da ta tabbatar, ta ce hukumar ta dinga tura gayyata ga tsohon gwamnan zuwa ofishinta dake Abuja saboda harkallar wasu kudade amma ya ki zuwa.
Okorocha, wanda yanzu sanata ne, ya ki zuwa gayyatar da aka yi masa, lamarin da ya fusata hukumar EFCC din kuma suka san hanyar kama shi.
A halin yanzu, hukumar EFCC na tuhumar dan siyasan a hedkwatarta kuma babu tabbacin ko za a bar shi ya tafi gida a yau din nan.
Bayanai a kan zargin da ake wa sanatan har a yanzu basu da yawa amma majiyoyi sun tabbatar da cewa suna da alaka da wasu kudade da suka bace yayin da yayi shekaru takwas a matsayin gwamnan Imo.
An kasa samun mai magana da yawun Okorocha, Sam Onwuemeodo, har a yammacin Talata kafin rubuta wannan rahoton.
A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana hannun hukumar.