EFCC ta Kama Wanda Suka Sace Wa Wani Attajiri Sama da Biliyan 1.5
An yi wa fitaccen Attajirin nan, Prince Arthur Eze, satar makudan kudi.
Ana zargin wasu ‘yan gida daya ne da su kayi aiki da shi da wannan laifi.
EFCC tace kudin da aka sace daga hannun Attajirin sun haura Biliyan 1.5.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta gurfanar da wasu ‘yanuwan juna da laifin yi wa Prince Arthur Eze.
Ana zargin Eze Okwuchukwu Olisaebuka da Eze Nnadozie Onyeka da kamfanoninsu da laifin satar N1.5b daga uban gidansu, Prince Arthur Eze.
A jawabin da hukumar EFCC ta fitar, ta nuna cewa an gurfanar da Okwuchukwu Olisaebuka da Eze Nnadozie Onyeka a kotun tarayya da ke Abuja.
Lauyoyin EFCC su na zargin wadannan mutane da aka ce ‘yan gida daya ne da laifin yin sata.
EFCC ta jefi Okwuchukwu Olisaebuka da kamfaninsa na Berlus Resources Ltd da zargin aikata laifuffuka 17.
Read Also:
Daga cikin manyan laifuffukan da ake zargin wannan mutumi akwai satar N804, 360, 216.81 da $3,309,359.08 daga dukiyar ‘dan kasuwa Prince Eze.
Shi kuma Nnadozie Onyeka wanda shi ma ya yi aiki da attajirin, ana zargin cewa ya wawuri kudi N769, 161, 690, $845,700 da £80,200 daga hannunsa.
Duka wadannan mutane da ake zargi ba su amsa laifinsu ba, Alkali ya bada belin Okwuchukwu Olisaebuka a kan miliyan 10, Onyeka a kan miliyan 20.

Alkali mai shari’a ya dakatar da cigaba da sauraron wannan kara a ranar Laraba, ya sa ranar 26 ga watan Junairu, 2021, domin a fara gudanar da shari’a.