Shin da Gaske ne, EFCC ta Kama Sanata Umar Tanko Al-Makura da Matarsa ?

 

EFCC ta kama tsohon gwamnan jahar Nasarawa Tanko Al-Makura da matarsa.

Majiyoyi daga EFCC sun bayyana cewa an kama shi ne bisa zargin bannatar da kudi da cin amanar jahar yayin da ya ke gwamna.

Danjuma Joseph, ya ce bai da masaniya a kan cewa EFCC ta kama mai gidansa a yayin da ake tuntube shi.

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jahar Nasarawa kuma sanata mai ci a yanzu, Tanko Al-Makura da matarsa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaidawa Premium Times cewa a halin yanzu jami’an EFCC na yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja.

Duk da cewa ba a samu cikaken bayani kan dalilin kama tsohon gwamnan da matarsa ba, majiyoyi sun ce kamun na da nasaba da zargin cin amana da bannatar da kudade da gwamnan yayi yayin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan Nasarawa.

Al-Makura ya rike mukamin gwamnan Nasarawa daga 2011 zuwa 2019 kafin aka zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a jahar.

Da aka tuntube shi game da batun, kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya ce kawo yanzu ba a masa bayani a kan lamarin ba.

Mene tsohon kakakin Al-Makura ya ce game da lamarin?

Tsohon mai magana da yawun gwamnan, Danjuma Joseph, ya ce bai da masaniya a kan lamarin a yayin da ake tuntube shi.

Joseph ya ce:

“Mai girma ya bar Lafia (babban birnin jahar Nasarawa) a safiyar yau don zuwa Abuja.

Bani da labarin an kama shi.”

Hukumar ta EFCC bata taba bincikan tsohon gwamnan ba a baya.

Hasali ma, hukumar ta EFCC ta taba taimakawa gwamnan da iyalansa a lokacin da wani dan damfara ya ya yi kokarin damfarar gwamnan a 2018.

Saurari karin bayani…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here