Hukumar EFCC ta Kama ‘Yan Yahoo 23 a Sokoto
Jami’an hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) sun kama wasu matasa 23 bisa zargin zambatar mutane ta intanet da aka fi sani da ‘Yahoo” a jihar Sokoto da ke arewacin ƙasar.
Gidan Talbijin na ƙasar NTA ya ambato mai magana da yawun hukumar reshen jihar Sokoto Kamal Ibrahim na cewa sun kama mutanen bayan samun bayan sirri kan ayyukan da suke aikata.
Read Also:
EFCCn ta ce jami’anta sun riƙa lura da bin sawun harkokokin matasan, inda suka gano suna rayuwa fiye da abin da yakamata ace suna samu a sana’o’in da suke iƙirarin gudanarwa.
An dai kama matasan ne da maraicen ranar Juma’a a rukunin gidajen Bafarawa da ke garin Sokoto da rukunin gidajen Kalkalawa da ke yankin Kalkalawa a jihar, inda a yanzu suka hannun hukumar domin ci gaba da gudanar da bincike.
Abubuwan da aka kama matasan da su, sun haɗar da ƙananan kotoci guda biyu da kwamfutoci da injin bayar da hasken lantarki da mayan wayoyin hannu 30.
Hukumar ta ce za ta gabatar da su a gaban kotu da zarar ta kammala gudanar da bincike a kansu.