EFCC ta Kara Gurfanar da Babachir David Karo na Biyu

 

A karo na farko tun bayan mutuwar Jastis Jude Okeke, EFCC ta sake gurfanar da Babachir David Lawal.

An fara gurfanar da Babachir, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, a watan Fabarairu na shekarar 2019.

EFCC na tuhumar Babachir da yin amfani da ofishinsa wajen bawa kamfaninsa kwangilar cire ciyawa a kan N544m.

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, tare da sauran wasu mutane Shidda, bisa zarginsu da badakalar N544m.

EFCC ta na zargin Babachir, da sauran mutanen, da yin amfani da matsayinsa wajen bawa kamfaninsa kwangilar cire wata shu’umar ciyawa a sansanin ‘yan gudun hijira (IDP) a kan kudi har miliyan N544.

Sai dai, Babachir da sauran mutanen da aka gurfanar sun ce basu aikata laifukan da ake tuhumarsu da su ba a cikin takardar kara da aka karanta a gaban Jastis Charles Agbaza, alkalin babbar kotun tarayya da ke Jabi a Abuja.

Wannan shine karo na biyu da aka gurfanar da Babachir da sauran wadanda ake tuhuma bayan mutuwar Jastis Jude Okeke, tsohon alkalin da ke sauraron karar, wanda ya mutu ranar 4 ga watan Agusta, 2020.

An fara gurfanar da Babachir, dan uwansa; Hamidu Lawal, Apeh Monday, da wasu kamfani guda biyu, a gaban marigayi Jastis Okeke a ranar 13 ga watan Fabarairu na shekarar 2019.

A ranar da aka fara zama domin fara sauraron shari’ar a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2019, lauya mai gabatar da kara ya bukaci kotu ta bashi lokaci domin sake tsara jadawalin tuhuma 10 da ake yi wa Babachir dangane da badakalar kwangilar N544m.

Hukumar EFCC ta fara kiran shaidunta a gaban kotu bayan ma su laifi sun yi gardamar amsa laifukansu.

Sai dai, kafin a kammala zaman sauraron gabatar da shaidun ne sai Jastis Okeke ya rasu.

Bayan rasuwar Jastis Okeke ne sai aka mayar da sharia’ar hannun Jastis Agbaza wanda ya fara sauraron shari’ar a karon farko ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here