EFCC: Ba Maina Kadai Bane ya Dibi Kudin Fansho

Wata Rouqquaya Ibrahim ta shaida wa babbar kotun tarayya cewa ba Maina kadai bane ya saci kudin fansho.

Bincike ya nuna Maina da wani ma’aikacin hukumar, Stephen Oronsaye ne suka saci naira biliyan 14 cikin kudin fansho.

Sun bude asusun bankuna fiye da 60 ba tare da amincewar akawu janar ba, suna kwasar kudade suna diddilasu ciki.

Wata shaida ta ce Abdulrasheed Maina, tsohon Shugaban hukumar fansho, ya saci naira biliyan 14 cikin kudin fansho tare da wani tsohon ma’aikacin hukumar.

Rouqquaya Ibrahim ta sanar da babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa Maina da Stephen Oronsaye, wanda shine shugaban ma’aikata tsakanin 2009 zuwa 2010, sun saci kudi kimanin naira biliyan 14 sun yita zuba wa a asusun bankuna fiye da 60.

Dama EFCC ta maka karar Maina a kan zargin satar naira biliyan 2, jaridar The Cable ta ruwaito. Alkali mai shari’a, Okon Abang, ya umarci cigaba da shari’ar bayan kin zuwan Maina kotu tun bayan bayar da belinsa.

A ranar Laraba, Ibrahim, shaida ta 9, wacce take daya daga cikin masu binciken EFCC, ta ce a bisa binciken da tayi, ta kama Abdulrasheed Maina da laifin satar kudin fansho mai yawa.

Kamar yadda shaidar tace, bincike ya bayyana yadda Maina yayita kwasar kudaden fansho yana diddilawa a asusun bankuna fiye da 60 wadanda Oronsaye ya bude.

Tace ofishin akawun gwamnatin tarayya ya tabbatar da babu amincewarsu wurin bude asusun ta ofishin Stephen aka budesu. Ta bude asusun bankuna 66 ba tare da amincewa ba.

“Bincike ya tabbatar da yadda Stephen Oronsaye yayi ta bude asusun bankuna 66, wanda su ka yi ta amfani dasu wurin satar kudaden fansho suna zubawa a cikinsu, akalla kudaden sun kai naira biliyan 14,” tace.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here