Damfarar Akanta Janar: EFCC ta Sako Babban Hadimin Gwamna Zulum

Hukumar yaki da almundahana tare hana yiwa tattalin arzirkin kasa zagon kasa ta sako babban hadimin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, wanda ta cafke.

Kamen yazo ne bayan wata wallafa da ya yi inda ya ce ana jita-jitar wani fitaccen ‘dan majalisa daga Borno na da alaka da damfarar N80 biliyan da akanta janar na tarayya ya sace.

Majiya ta ce, gwamna Zulum ya kira shugaban EFCC na yankin tare da jin ba’asin da yasa suka rike babban hadimin nasa, inda suka yi alkawarin sakinsa a safiyar Juma’a.

Borno – Hukumar yaki da cin hanci tare da hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa ta saki Abdullahi Yusuf, babban hadimin Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno.

Yusuf ya yi wallafa a ranar 29 ga watan Mayu, inda yake cewa ana jita-jitar wani fitaccen ‘dan majalisa daga Borno na da alaka da damfarar N80 biliyan da ke da alaka da Ahmed Idris, akanta janar na tarayya.

Duk da dai hadimin bai ambaci suna ba, magoya bayan ‘dan majalisar da ke wakiltar mazabar Biu sun je karkashin wallafar tare da zargin da ‘dan majalisar ya ke, The Cable ta rawaito.

Saboda haka ne EFCC suka gayyaci Yusuf ofishinsu na Maiduguri.

An ruwaito yadda ya isa ofishin EFCC washe garin ranar daga bisani suka tsare shi, duk da irin yadda iyalinsa suka yi kokarin ganin an sako shi amma abun ya gagara.

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, an sako Yusuf a ranar Juma’a bayan Zulum ya sa baki.

Gwamnan ya kira shugaban ofishin EFCC na yankin, tare da neman sanin ba’asin da yasa aka rike hadimin. “Ubangidanmu ya bayyana mana yadda gwamna ya kira sa a kan kama Yusuf da aka yi. Ran gwamnan ya matukar baci,” a cewar majiyar.

“A takaice dai, ubangidanmu ya ce gwamnan ya so zuwa ofishin don ya hadu da Yusuf, kafin shugaban yankin ya bashi tabbacin za a sake shi a safiyar Juma’a.”

Haka zalika, EFCC ta maka Yusuf babban kotun tarayya bisa karya dokar tattalin arzirkin ta 2004. Sai dai, hadimin bai gurfana ba kafin a sako shi ranar Juma’a.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here