Naja’atu Muhammad ta Bukaci EFCC tayi Bincike Domin Gano Kudin da Aka Fitar a PSC
Naja’atu Muhammad wanda kwamishina ce a hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta kai korafi.
Kwamishinar ta PSC ta sanar da hukumar EFCC cewa Musiliu Smith ya na satar dukiyar kasa.
‘Yar gwagwarmayar ta bukaci ayi bincike domin gano gaskiyar wasu kudi da aka fitar a PSC.
Abuja – Daily Nigerian ta ce Naja’atu Muhammad ta rubuta takardar korafi a ranar 29 ga wayan Yuni 2022, tana mai zargin shugaban PSC da badakala.
Muhammad mai wakiltar Arewa maso yamma a hukumar ta kasa tace Musuliu Smith yana bada kwangiloli ba tare da la’akari da dokokin kasa ba.
‘Yar siyasar tace tun da aka rantsar da kwamitin kula da hukumar a 2018, sau biyu aka yi zama. A cewar ta, Smith kadai yake cin kare babu babbaka.
An rahoto kwamishinar tana cewa shugaban na PSC ya bada kwangilar N34,749,375 ga kamfanin EMPLUG LTD na tsara shafin daukar aikin NPF.
Read Also:
A bayaninta, Naja’atu Muhammad tace Smith ya bada kwangilar ba tare da tuntubar kowa ba, sannan akwai ma’aikatan hukumar da suka yi aikin a kyauta.
Daga cikin korafin da ta gabatarwa EFCC shi ne PSC ta biya N36,228,453.90 ga Wedewood Integrated Investment Limited na kwangilar wani aikin ofis.
Baya ga haka, takardar da aka aikawa EFCC ta nuna yadda aka cire kusan N200m a 2021 daga asusun hukumar, aka rika aikawa kamfanin Vita Construction.
Har yau, Muhammad tace babu wanda ya san dalilin wadannan makudan kudi da aka fitar.
An bukaci EFCC tayi bincike domin gano ainihin abin da ya faru.
An kuma aikawa ma’aikacin hukumar mai suna Ogo Edward kudi har N7,000,000.00 domin sayen kayan COVID-19 da N25m da sunan tsaro wajen daukar aiki.
An fitar da miliyoyin alhali samar da tsaro nauyi ne da ya rataya a kan wuyar dakarun ‘yan sanda.
Abin bai kare a nan ba, Naja’atu ta zatgi Smith da amincewa a kashe N32m a matsayin kudin tafiya na DTA, aka tura duka kudin a asusun wani ma’aikacin PSC.
Sauran zargin badakalar sun hada da N15.4m na shirya taron ‘yan jarida da N104.49m na ayyka da aka bada ba tare da izini ba da kuma N91.99m na kwangila.