Damfara ta Yanar Gizo: Hukumar EFCC ta Kama Yaro da Mahaifiyarsa

 

Wasu ‘yan damfara sun shiga hannun hukuma bayan da suka aikata munanan laifuka.

An gano yadda wani matashi ya shigar da mahaifiyarsa harkar damfara ta yanar gizo.

Hakazalika, an gano wata daga cikin ‘yan damfarar da ta sayar da asusun ta na Facebook saboda aikata barna.

Kaduna – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a shiyyar Kaduna ta cafke wasu mutane hudu da suka hada da Lucky Ebhogie, Richman Kas Godwin, Israel Justin da Precious Iwuji da aikata laifin zambar ta yanar gizo.

An damke su ne a ranar 5 ga Agusta, 2021, a unguwar Sabo da ke Kaduna, a Jahar Kaduna biyo bayan bayanan sirri kan zarginsu da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo, Daily Nigerian ta ruwaito.

Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin galibi suna da hannu cikin aikata zamba da kulla soyayyar karya soyayya; yin karya da sunan ma’aikatan sojin Amurka akan ayyukan kasashen waje don yaudarar mutanen da suka fada fatsarsu.

Daya daga cikin wadanda ake tuhuma, Lucky Ebhogie ana zargin ya tsoma mahaifiyarsa, Margaret Sylvester, cikin damfarar ta hanyar amfani da asusunta don aikata laifi.

A ranar 30 ga Yuli, 2021, ya sayi mota kirar Mercedes Benz GLK akan kudi Naira miliyan 7 ta asusun bankin mahaifiyar tasa.

Wata wacce ake zargi, Precious Iwuji an gano cewa ta sayar da hotunan ta da asusun ta na Facebook ga masu damfara ta yanar gizo, wanda suke amfani da shi wajen dasa tarko kan jama’a.

Nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargi zuwa kotu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here