IG Egbetokun ya Umarci Jami’an ƴan Sanda da su kare Masu Zanga-Zanga
Babban sufeton ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya umarci manyan jami’an ƴan sanda da su kare waɗanda suka shirya zanga-zanga kan adawa da tsadar rayuwa daga ranar 1 ga watan Agusta.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata wasika da Sufeto Janar ɗin ya aika kan buƙatar wani lauyan kare hakƙin ɗan’adam Ebun-Olu Adegboruwa.
Read Also:
A ranar 26 ga Yulin 2024, Adegboruwa ya rubuta wa Sifeton ƴan sandan wasika domin ya buƙaci ƴan sanda su bayar da kariya ga masu zanga-zangar.
Babban lauyan ya dai rubuta wasiƙar ne a madadin ƙungiyar ‘Take It Back’, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke shirya zanga-zangar.
A cikin wasikar martani mai ɗauke da sa hannun CP Johnson Adenola, Egbetokun ya umurci manyan jami’an ƴan sanda da su saurari buƙatun babban lauyan.
Ya kuma buƙaci gana wa da Adegboruwa a Abuja a ranar Talata, 30 ga watan Yuli, 2024, domin a ci gaba da tattaunawa kan buƙatarsa.