Tashin Fetur: Gwamnatin Ekiti ta Rage wa Ma’aikata Ranakun Zuwa Aiki

Jihar Ekiti – Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya amince ma’aikata su rika zama suna aiki daga gida a wasu kwanakin mako.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne domin ragewa ma’aikata raɗaɗin wahala da tsadar rayuwar musamman bayan ƙara tashin farashin man fetur.

Mai magana da yawun gwamnan, Mr Yinka Oyebode shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Gwamna ya tsara ranakun zama a gida Sanarwar ta ce Gwamna Oyebanji ya amince ma’aikatan da ke mataki na 1 zuwa 7 su zauna a gida su yi aiki na ranaku uku, ma’ana sau biyu za su fito aiki a mako.

Kazalika ma’aikatan da suka kai mataki na 8 zuwa 12 za su zauna su yi aiki daga gida na kwana biyu, su fito wurin aiki a sauran kwanakin aiki uku.

Sai kuma ma’aikatan da suka kai mataki na 13 zuwa 17 za su yi aiki daga gida na kwana ɗaya, sannan su rika fitowa aiki na sauran ranaku huɗu a mako.

Yaushe sabon tsarin zai fara aiki?

Sabon tsarin zai fara aiki daga ranar Litinin, 9 ga Satumba, 2024, amma ban da ma’aikata masu mahimmanci kamar malamai, ma’aikatan lafiya da sauransu.

Gwamnan ya umarci kowace ma’aikata ta zauna ta tsara jadawalin aiki ta yadda sabon tsarin aiki a gida ba zai kawo tasgaro a ayyukan da gwamnati ta sa a gaba ba.

Oyebanji ya ce za a tafi a wannan tsarin na watanni biyu kuma bayan haka gwamnati za ta sake nazari kafin a ci gaba ko a dakatar da shi, rahoton Punch.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here