El-Rufai ya Shawarci ECOWAS da ta Dakatar da Shirin Amfani da ƙarfin Soji a Jamhuriyar Nijar

 

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shawarci Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta dakatar da shirin amfani da ƙarfin soji a Jamhuriyar Nijar.

A wani saƙo da El-Rufa’i ya wallafa a shafinsa na X, wato Tuwita a yau Talata, ya bayyana mazauna Arewacin Najeriya da Nijar a matsayin ƴan’uwan ​​juna.

Ya ce “Tabbas mutanen Nijar abu ɗaya ne kuma al’umma ɗaya ce da na Arewacin Najeriya. Ya kamata mu kauce wa wannan yaƙin basasa tsakanin ƴan’uwa.”

Tsohon gwamnan ya yi wannan gargadin ne biyo bayan sanarwar da shugabannin tsaro na kungiyar ECOWAS ta yi cewa sun shirya yin amfani da karfin soji a Nijar domin dawo da habararren shugaban kasar, Muhamed Bazoum kan mulki.

A taron da suka yi na ƙarshe a ƙasar Ghana, Manyan hafoshin dakarun Ecowas sun ce sun tsayar da ranar da za su tura dakaru zuwa Nijar domin tunkarar gwamnatin mulkin Janar Abdoulrahamane Tchiani domin dawo da mulkin demokuradiyya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com