Emefiele ya Musanta Sabbin Tuhume-Tuhume da EFCC Take Masa
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya musanta aikata tuhume-tuhume 20 da hukumar EFCC mai yaki da yi wa arzikin kasa ta’annati take masa wadanda aka sabunta.
Read Also:
A yanzu tuhume-tuhumen da ake yi wa Emefiele sun hada da zargin cin amana da zamba da hada baki wajen aikata babban laifi da jabu.
Tsohon gwamnan babban bankin wanda aka ba shi beli ya samu izinin fita daga Abuja amma ba kasar ba kamar yadda alkali Hamza Muazu na babbar kotu a Abuja ya yanke.
Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo bai kalubalanci hukuncin ba shi beli ba.
Da yake amincewa da bukatar ba da beli, Alkali Muazu ya dage karar zuwa 12 da 13 ga watan Fabarairu domin ci gaba da zama.