Kungiyar da ta fi ESN/IPOB Hatsari ta Shiga Jahar Imo

 

Sabuwar kungiyar yan tada kayar baya ta bulla a jahar Imo, yanƙin kudu maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyar mai suna Biafran Motherland Warrior ta fi ESN/IPOB hatsari.

Mayakan kungiyar sun fara kai hari ga jami’an tsaro a yankin Mbaise, jahar Imo.

Imo – Wata sabuwar ƙungiyar yan bindiga mai suna ‘Biafran Motherland Warrior’, ta bayyana yankin kudu maso gabashin Najeriya, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Rahoto ya nuna cewa sabuwar ƙungiyar ta fi sojojin ESN na haramtacciyar ƙungiyar yan aware IPOB hatsari.

A yanzun sabuwar kungiyar BMW ta fara kai hare-haren ta a yankin Mbaise dake jahar Imo, kudu maso gabashin Najeriya.

Wani sabon bidiyo da ya mamaye kafafen sada zumunta, ya nuna yadda mayakan kungiyar suke kai hari kan jami’an tsaro a Mbaise.

Shin jami’an tsaro na da masaniya kan kungiyar?

Wakilin dailytrust ya gano cewa mutanen dake yankin sun sanar da ayyukan da sabuwar kungiyar ke aiwatarwa a yankin.

Duk da cewa ba komai ne ya fito fili game da su, amma rahoto ya tabbatar da cewa mayakan kungiyar sun maida hankali ne wajen kaiwa jami’an tsaro hari.

Duk kokarin da akai na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Imo, ASP Mike Abattam, ya ci tura domin yaki ɗaga kiran wayar da akai masa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here