Cin Kasuwanni Mako-Mako: Gwamnatin Jahar Kaduna ta Dakatar da Kananan Hukumomi Biyar

 

Gwamnatin Jahar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta dakatar da cin kasuwanni mako-mako a wasu kananan hukumomi biyar na Jahar.

An kuma haramta wa gidajen mai sayar da mai a jarka tare da haramta sayar da man a gefen titi.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Jahar Zamfara ta dauki irin wannan mataki a fadin jahar baki daya.

Samuel Aruwan kwamishinan tsaro da harkokin cikin na Jahar Kaduna ya shaida wa BBC cewa an dauki matakin ne a kananan hukumomin guda biyar saboda dalilai na tsaro.

Kananan hukumomin da matakin ya shafa sun hada Birnin Gwari da Igabi da Giwa da Kajuru da Chikun.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here