Fada ya Kaure Tsakanin ƙungiyoyin Ƴan Bindiga, Ƴan Ta’adda 20 Sun Mutu

 

Katsina – Wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga masu adawa da juna sun yi artabu a jihar Katsina, akalla ƴan ta’adda 20 sun baƙunci lahira.

Rahotanni sun nuna ƴan bindigar sun kaure da faɗa tare da karkashe junansu da safiyar ranar Laraba a kauyen Ɗan Ali da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a Katsina.

Masani kuna mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

An kashe ƴan bindiga 20 a jihar Katsina

Ya ce ya samu labarin daga cikin waɗanda suka mutu a arangamar har da wasu daga cikin jagororin ƴan ta’addan.

Ya ƙara da cewa faɗan ya faru ne tsakanin ƙungiyar ƴan bindiga karkashin Mai Nore da mayakan kungiyar Buzaro.

“Da sanyin safiyar yau (jiya Laraba), wani kazamin fada ya barke tsakanin kungiyar ƴan bindiga ta Mai Nore da kungiyar Buzaro a yankin Dan-Ali.

“A cewar wasu majiyoyin leken asiri, faɗan ya zama silar rage mugun iri, inda aka samu gawarwakin ƴan bindiga sama da 20 a wurin.”

– Zagazola Makama.

Yadda ƴan bindigar suka yaƙi juna

Ganau da suka ga abin da ya faru sun ce faɗan da ƴan ta’addan suka yi a tsakaninsu ya yi tsanani sosai domin an riƙa jin ƙarar harbe-hare a ilahirin yankin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojojin Najeriya ta ƙara matsa ƙaimi wajen kakkaɓe ƴan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here