Sakataren Fadar Shugaban Kasa ya Shaida wa Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Karancin Kudi da Fadar Ke Fuskanta
Fadar Shugaban kasar Najeriya ta na korafin cewa ta na fama da karancin kudi.
Sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasar ya ce ba su samun isassun kudi.
Tijjani Umar ya bayyana wannan a lokacin da Sanatoci suka kawo masu ziyara.
Abuja – Gazawar fadar shugaban kasa na samun kudin da aka ware mata a kasafin kudin kasa ya na jawo wa Aso Villa matsala wajen aiwatar da ayyuka.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Tijjani Umar ya yi wannan bayani a ranar Lahadi, 9 ga watan Agusta, 2021.
Kwamitin Majalisa ya ziyarci Fadar shugaban kasa
Babban sakataren ya shaida wa kwamitin majalisar dattawa kan harkokin gwamnati da daidaiton mukamai cewa abubuwa suna sukurkuce masu.
Read Also:
Malam Tijjani Umar ya zagaya da kwamitin Sanatocin da suka ziyarci fadar shugaban kasar domin ganin aikin sabon asibitin manya da ake gina wa.
Ana sa ran cewa za a kammala aikin wannan asibiti kafin gwamnati Muhammadu Buhari ta bar mulki.
Shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya jagoranci ma’aikatan fadar shugaban kasan da suka tarbi kwamitin ‘yan majalisar.
Babu isasshen kudi a fadar shugaban kasa
Da yake magana a karshen makon jiya a kan kalubalen da fadar shugaban kasa ta ke fuskanta, Umar ya ce rashin wadattacen kudi ya na zama masu cikas.
Umar ya ce Naira biliyan 5.083 fadar shugaban kasa ta samu daga cikin Naira biliyan 8.699, watau 58% da aka ware mata a cikin kasafin kudin shekarar 2019.
A shekarar 2019, jami’in gwamnatin ya ce Naira biliyan 6.955 aka ware wa fadar shugaban kasa, amma Naira biliyan biyu rak (kusan 38%) su ka iya fito wa.
Amma an yi dace, a shekarar da ta gabata, duka kudin da aka ware wa fadar shugaan kasar sun fito.