Da Fadin Cigaba a Baki Zai Kawo Cigaba, da Mun Kasance Kasa Mafi Cigaba a Duniya – Tinubu
Jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata yan Najeriya su fadawa juna gaskiya.
Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana niyyar takarar kujeran shugaban kasa a zaben Febrairun 2023.
Tinubu ya bada kyautar cibiyar karatu na kimanin kudi biliyan daya ga jami’ar jihar Legas LASU.
Legas – Mai niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa dukkanmu muka kashe Najeriya kuma mu zamu iya gyarata.
Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a lakcan bikin yaye daliban jami’ar jihar Legas LASU.
Ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar Legas, Dr Obafemi Hamzat, rahoton Vanguard.
Yace:
Read Also:
“Mu daina yaudarar kawunanmu. Mun dade muna ikirarin cewa muna da arziki kuma gobe zamu ji dadi amma shekaru na taf iya kuma babu cigaba.”
“Da fadin cigaba a baki zai kawo cigaba, da mun kasance kasa mafi cigaba a duniya.”
“Amma kash, Najeriya na waje guda. Mun zama masu fitar da dukiyarmu amma mu shigo da kaya da tsada.”
“Wajibi ne mu fadawa juna gaskiya, mu fuskancesa mu gyara. Dukkan mu muka janyo kuma zamu iya zama mafita. Mu hada kai. Wajibi ne mu gyara kasar nan.”
A kan rashin aikin yin matasa, Tinubu ya ce rashin aiki da aiki babu albashin kwarai tsakanin matasa ya kai 60%, kuma wajibi ne a magance hakan.
Tinubu yace samawa matashin birane aikin yi, aikin noma, harkar gidaje, ilimi, tattalin arziki da manyan ayyuka ya kamata gwamnati ta mayar da hankali.
Tinubu ya bada kyautar cibiyar karatu na kimanin kudi biliyan daya ga makarantar.