Abdulrasheed Bawa: Farfesa Isa Pantami ya Alaƙanta Faɗuwar da Takurawa Kai da Kuma Yawan Aiki
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya bayyana dalilin da yasa shugaban EFCC ya yanke jiki ya faɗi.
Abdulrasheed Bawa ya yanke jiki ya faɗi ne yayin da yake jawabi a fadar shugaban ƙasa, an gaggauwa bashi agajin gaggawa.
Pantami ya alaƙanta faɗuwar bawa da takurawa kansa da yayi da kuma ayyukan da suka masa yawa.
Abuja – Babban dalilin da yasa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya yanke jiki ya faɗi yayin da yake jawabi a fadar shugaban ƙasa ya fito fili.
Vanguard ta rawaito cewa Bawa, wanda ya matsa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ya yanke jiki ya faɗi yau Alhamis.
Read Also:
Rahoto ya nuna cewa an yi gaggawar kai shugaban EFCC zuwa asibitin dake cikin Aso Rock domin samun agajin lafiya cikin gaggawa.
Da yake martani kan lamarin, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Pantami, ya alaƙanta faɗuwar da takurawa kai da kuma yawan aiki.
Ministan ya yi kira ga yan Najeriya su saka Bawa cikin addu’o’insu, ya bayyana cewa shugaban ya samu kulawar da ta dace kuma ya dawo hayyacinsa.
Wane hali Bawa yake ciki?
Bayan wasu yan mintuna da kai Bawa asibitin cikin Aso Rock, Kakakin hukumar EFCC, Mr. Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa shugabansu yana cikin koshin lafiya.
Kakakin EFCC yace:
“Shugaban EFCC, Albdulrasheed Bawa, yana cikin koshin lafiya. Bayyana haka ya zama wajibi biyo bayan abinda ya faru a yau 16 ga watan Satumba, a fadar shugaban ƙasa, lokacin da yake jawabi.”
“Bayan abinda ya faru, Bawa ya samu kulawar lafiya cikin gaggawa kuma tuni ya koma kan kafafunsa.”