Ba za a Fahimci Tasirin Ayyukan da Nake yi ba Sai Bayan na Sauka – Shugaba Buhari

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba za a fahimci tasirin ayyukan da yake yi ba, sai bayan ya sauka daga mulki a shekara ta 2023.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin naɗin sabbin shugabannin hukumar kula da asusun zuba jarin ƙasashen waje a Najeriya wato NSIA, kamar yadda jaridar Daily Trust ta Najeriya ta rawaito.

A wani gajeren biki da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, Buhari ya bukaci sabbin shugabannin su mayar da hankali wajen ganin an sake samun kari a zuba hannayen jari da za su taimaka wajen tayar da komaɗar tattalin arziki, yayin da ake hasashen farashin ɗanyen mai zai faɗi zuwa dala 40 kan kowacce ganga kafin shekara ta 2030.

Shugaban ya jaddada matsayin gwamnatinsa na kirkiro ayyukan dogon-zango da shirye-shirye da za su samar da ayyuka a Najeriya.

Kuma yana mai cewa ba za a fahimci tasirin ayyukan da yake bijiro da su ba a yanzu sai lokacin da ya bar mulki, saboda tsare-tsarensa da ayyukansa na dogon-zango ne.

Buhari ya ce babu shakka wannan sauyin da suke faɗi za su faru amma ba kamar yadda wasu ke tsammani ba wato a lokaci guda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here