Cif Femi Falana ya yi Kira ga Ministan Shari’a da ya Aiwatar da Bukatar Amurka Akan Mika Kyari

 

Babban Lauya, kuma dan rajin kare hakkin dan adam Femi Falana, ya nemi a mika Kyari ga FBI.

Ya ce, ya kamata rundunar ‘yan sanda ta yi bincike mai zurfi sannan ta kai Kyari Amurka a bincikeshi.

Ya bayyana haka yayin da aka tambaye shi ra’ayinsa game da dambarwar da ake zargin Abba Kyari akai.

Shahararren lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan adam, Cif Femi Falana (SAN) ya yi kira ga Babban Lauyan Tarayya (AGF) kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya aiwatar da bukatar Amurka ta mika mata Abba Kyari akan ka’ida.

Kyari, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jahar Borno, kwanan nan ne Hukumar Bincike ta FBI, wata hukumar tabbatar da doka a Amurka ta zarge shi da hannu a wata harkallar damfara.

Ramon Abbas (Hushpuppi) wanda ake zargi da damfarar wani hamshakin attajiri, ya furta cewa ya ba Kyari cin hanci don kamo wani da ya nemi ya zarce shi a zambar dala miliyan 1.1.

Wannan fallasa ta girgiza ‘yan Najeriya da yawa kamar DCP Kyari kafin yanzu, wanda aka fi sani da Jarumin Dan Sanda na Najeriya.

A matsayinsa na Shugaban Rundunar Bayar da Bayanan Sirrin ‘Yan Sanda (IRT), tawagar Kyari ta kware wajen cafke dimbin masu aikata laifuka a cikin kasar wanda hakan ya ba shi yabo a zaman majalisa na musamman daga Majalisar Wakilan Najeriya.

Falana ya ce dole ne Najeriya ta mutunta yarjejeniyar kasa da kasa.

Falana ya ce Kwamitin Bincike na Musamman da Babban Sufeto Janar ya kafa Babban Sufeto kan lamarin da ake dubawa ya kamata ya yi cikakken aiki.

Da yake magana yayin wata hira ta wayar tarho da gidan Talabijin na Afirka mai zaman kansa wanda jaridar Daily Sun ke sa ido, Falana ya bayyana cewa Kyari ya samu ne daga tsarin gwamnatin da ya gaza.

A kalmomin sa yake cewa:

“Don kawo karshe da rufe wannan mummunan babi, binciken dole ne ya wuce tuhumar da FBI ta yi, dole ne a bincika lamarin a cikin gida, kuma ba wai a mika Kyari ga Amurka kawai ba.

“Muna aiki a karkashin doka ko gwamnati ta so ko ba ta so, akwai dokar mika mutum wanda kasashe kamar Amurka da Najeriya suka kulla yarjejeniya da su.

“Don haka akwai hanyoyin da za a bi idan ana son wanda ake zargi da laifi a nan ko a Amurka ya fuskanci shari’ar kotu.

“Game da Najeriya-Amurka, an shiga yarjejeniya a 1935 karkashin mulkin mallaka na Burtaniya, kuma tsakanin lokacin zuwa yanzu, an mika dimbin ‘yan Najeriya, wasu an karbe su an jefar dasu a Amurka, amma ba ko guda daya, wanda ake zargi Ba’amurke da aka kawo shi kotu a Najeriya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here