A Shirye Muke mu Fara Biyan Bashin Alawus Din N-Power – Akindele Egbuwalo

 

Gwamnatin Tarayya ta ce a shirye ta ke ta fara biyan basusukan da wadanda ke shirin N-Power ke bin ta.

Masu kula da shirin na N-Power ne suka sanar da hakan yayin taro da wasu masu amfana da shirin a taron a Abuja.

Legit.ng ta rahoto cewa an kirkiri shirin na N-Power a ranar 8 ga watan Yunin 2016, karkashin gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, domin magance matsalar karancin ayyukan yi da kuma inganta walwala da cigaba.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba, ta ce za ta fara biyan bashin alawus dinsu na watanni 9 a Nuwamban 2023.

Manajan shirin N-Power na kasa, Akindele Egbuwalo ne ya bayyana hakan a cewar The Nation.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com