Majalisar Dattawa na Tantance Sabon Shugaban Hukumar EFCC

 

Majalisar datawa na tantance waɗanda shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ola Olukoyede; da Sakataren Hukumar, Muhammad Hammajoda.

A ranar 12 ga watan Oktoban 2023 ne shugaban ƙasar ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar kuma Muhammad Hammajoda a matsayin sakataren hukumar har sai majalisar dattawa ta tabbatar da su.

A ranar 14 ga watan Yunin 2023, Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar don ba da damar gudanar da bincike mai kyau a kan yadda ya ke aiki a lokacin da yake shugabancin hukumar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com