Gwamnatin Tarayya Za ta Fara Biyan Dalibai Masu Karatun Digiri da NCE Alawus
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, za ta fara biyan dalibai kudin alawus na karatu a manyan makarantu.
Wannan na zuwa daga ma’aikatar ilimi ta tarayya yayin bikin tunawa da ranar malamai ta duniya.
Gwamnati ta bayyana yadda ta tsara abin, inda ta ce za a biya masu karatun NCE N50,000 masu karatun digiri kuma N75,000.
Abuja – Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan N75,000 a matsayin alawus-alawus na kowane semester ga daliban da ke karatun digiri a fannin Ilimi a jami’o’in gwamnati a Najeriya, Punch ta rawaito.
Read Also:
Hakanan, daliban NCE za su karbi N50,000 a matsayin alawus na kowane semester a wani kokarin gwamnati don jawo hankalin samar da kwararrun malaman makaranta kamar yadda Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya yi alkawari shekaran da ya gabata.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba, a bikin ranar malamai ta duniya da aka gudanar a Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja.
Adamu, wanda Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Sonny Echono ya karanta jawabinsa a taron, ya ce ma’aikatarsa za ta hada kai da gwamnatocin jahohi don tabbatar da samar da aikin yi ga daliban kai tsaye kan kammala karatun.
Ya ce:
“Daliban digiri na B.Ed/B.A.Ed/ BSc.Ed a cibiyoyin Gwamnati za su karbi alawus na N75,000.00 a kowane semester yayin da daliban NCE za su sami N50,000.00 a matsayin alawus a kowane semester.
“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta nemo hanyar da gwamnatocin jahohi za su iya ba da aikin yi ga masu wadanda suka kammala NCE a matakin Ilimi na farko.”