Sarkin Musulmai ya Umarci Al’umma da Su Fara Duba Sabon Watan Rajab Daga Daren Gobe
Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa’ad Abubakar ya umurci mutane su fara neman jinjirin watan Rajab.
Sarkin Musulmin ya bada sanawar ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Wazirin Fadarsa, Farfesa Sambo Wali.
Sanarwar ta umurci al’umma su fara duban jinjirin watan da zarar rana ta fadi a yau Alhamis Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nigeria, NSCIA, ta ce al’ummar musulmi su fara duba sabon watan Rajab a kalandar musulunci daga Juma’ar gobe, Aminiya ta ruwaito.
Read Also:
Sanarwar ta NSCIA da sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ke jagoranta ta ce Juma’a ce zata kasance 29 ga watan Jumadal Akhira wanda zai yi dai-dai da 12 ga watan Fabrairun shekarar 2021.
Kazalika, sanarwar ta umurci al’umma da su kai rahoton ganin jaririn watan ga dagaci ko mai unguwa mafi kusa da su domin isar da sakon da ganin jaririn watan gar Sarkin Musulmi.
Sanarwar wacce Wazirin Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Professor Sambo Wali Junaidu ya saka wa hannu ta ce a fara duban jinjirin watan bayan faduwar rana.
Watan Rajab shine na takwas cikin jerin watannin da ke kalandar Musulunci ta Hijra, mai biye masa kuma shine watan Ramadan.