Zaben 2023: An Fara Kafa Fastocin Tinubu
Hotunan neman takarar Asiwaju Bola Tinubu suna yawo a unguwannin Legas.
Magoya bayan Bola Tinubu suna baza fastocin 2023 a Ojota, Maryland, da Ikeja.
Bayan haka an ga wasu hotunan Tinubu a yankunan Ikorodu, Ikotun da Igando.
Lagos – Duk da cewa babban jigon jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, bai bayyana niyyar shiga takara ba, wasu na ta yi masa yakin zabe.
Jaridar Punch ta kawo rahoto cewa hotunan Asiwaju Bola Tinubu yana neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 sun fara zagaye garin Legas.
Rahotanni sun ce an ga fastocin tsohon gwamnan na jahar Legas a wasu unguwannin Legas kamar su Ojota, Maryland, Ketu Ikeja, da kuma Lagos Island.
Haka zalika an baza hotunan Tinubu a Ikorodu, Ikotun, Igando, da unguwar Ojuelegba, da sauransu.
Read Also:
Sai dai magoya bayan ‘dan siyasar da suka buga wadannan hotunan kamfe, ba su bayyana wanda ake sa rai zai yi wa Tinubu abokin takara a zaben na 2023 ba.
Kungiyar SWAGA’23 ta dage da kamfe
Bayan haka, kungiyar da tayi fice wajen yi masa kamfe, Southwest Agenda for Asiwaju, SWAGA’23 ta dage wajen wayar da kan mutane kan takararsa a Kudu.
Prince Dayo Adeyeye wanda ya yi aiki da Marigayi Moshood Abiola shi ne ya kafa wannan kungiya ta SWAGA domin ganin Bola Tinubu ya karbi mulki.
Jaridar tace Prince Adeyeye ya kaddamar da ofisoshin kamfe a Osun, Ogun, Ondo da Ekiti. Tun a karshen shekarar 2015 aka bude babban ofis a garin Ibadan.
Sarakuna suna tare da Tinubu a 2023 Irin wannan yunkuri ya sa Southwest Agenda for Asiwaju ta gana da sarakunan Legas a jiya.
Sarakunan da suka yi wa Tinubu mubaya’a a zaman da aka yi sun hada da Onigando na Igando, Oba Lasisi Gbadamosi, Ojora na kasar Ijora, Sarki Fatai Ojora.
Ragowar Sarakunan sune Oniru na Iruland, Oba Gbolahan Lawal, da Elegushi na kasar Ikateland.