Farashin Kayan Masarufi ya Haura Zuwa Kashi 27.33 Cikin 100 a Najeriya

 

Farashin kayan masarufi a Najeriya ya haura zuwa kashi 27.33 cikin 100 a watan Oktoban 2023, sakamakon hauhawar farashin kayayyakin abinci bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi.

Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar na Oktoban 2023 a ranar Laraba.

Rahoton ya nuna tashin farashin kayan masarufi daga 26.72 cikin 100 na watan Satumba 2023 zuwa 27.33 cikin 100 inda yake nuna ƙaruwar 0.61 cikin 100.

Bugu da ƙari, rahoton ya kuma yi nuni da cewa, hauhawar farashin kaya a duk shekara ya kai 6.24 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Oktoba na shekarar 2022 wanda ya kasance a kashi 21.09 cikin 100

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com