Farfesa Yusuf Turaki ya yi Magana Kan Najeriya

 

Shugaba a yankin tsakiyar kasar nan, Farfesa Yusuf Turaki, ya ce Najeriya tana dab da tarwatsewa.

Farfesan arewacin Najeriyan ya ce har sai an gyara kundin tsarin mulkin kasar nan ne za a gujewa hakan.

Turaki ya jajanta tsanantar rashin tsaro da ya addabi dukkan kasar nan da yadda hakan ke kamari.

Farfesa Yusuf Turaki ya ja kunne inda yace akwai yuwuwar Najeriya ta tarwatse a kowanne lokaci daga yanzu matukar aka cigaba da amfani da kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999.

A wata hira da yayi da jaridar The Sun, farfesan ya kwatanta kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da abinda ba zai kai kasar nan inda ake tsammani ba.

Turaki ya ce babu shakka kundin tsarin mulkin kasar nan yana daga cikin dalilan da suka hana kasar nan cigaba duk da shekaru 60 da tayi da samun ‘yancin kai.

Ya ce: “Abinda na gane shine abinda ke faruwa yanzu yana da tushe da babban tarihi wanda aka gina mana tuntuni.Ina tuna tarihin baya, yadda turawan mulkin mallaka suka kafa kasar nan da muke kira da Najeriya.

“A arewacin Najeriya, na yanke shawarar duba bangarori biyu,, na Musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba kuma na so duba yadda turawan mulkin mallaka suka gina dokokinsu.”

Turaki ya kwatanta kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da damfara a bayyane, kari da cewa duk wanda yace kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 abun alheri ne ga Najeriya toh son kan shi kawai yake.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here