Ba na Fargaba Kan Matakin da Tinubu Zai ɗauka Wajen Yin Garambawul a Gwamnatinsa – Musawa
Ministar fasaha da raya al’adu ta Najeriya, Hannatu Musawa, ta ce ba ta damu da batun shirin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ke yi ba na yin garambawul a majalisar zartarwarsa.
Ministar ta bayyana haka ne a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi.
An tambayi ministar ko tana fargabar Shugaba Tinubu zai iya cire ta idan aka yi la’akari da cecekucen da ya mamaye ta bayan ba ta muƙamin minista?
Read Also:
Sai ta ce: “Ba ni tunanin akwai wani cecekuce da ya dabaibaye naɗina da kuma ofishina. Abin da za ni ce shi ne, na yi wa Shugaba Tinubu kamfe domin ya zama shugaban ƙasa, saboda haka na amince da duk matakin da zai ɗauka.
“Ban damu ba saboda na san cewa ci gaban ƙasa ne a gaban shugaba Bola Ahmed Tinubu, don haka duk matakin da zai ɗauka wajen yin garambawul a gwamnatinsa zai zama mai amfani ga ƴan Najeriya.
An daɗe ana kiraye-kiraye ga shugaban Najeriya da ya sauya wasu daga cikin ministocinsa saboda ana ganin ba su yin abin da ya dace.
A ƙarshen watan da ya gabata, mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya ce shugaban ya bayyana kudurinsa na yin garambawul ga majalisar zartarwarsa, sai dai ba a bayyana lokaci ba.