Gwamnonin Arewa Ya Kamata Mu Farka Akan Rashin Tsaro – Zulum
Zulum ya bukaci gwamnonin yankinsa su tashi tsaye kafin rikicin yan bindiga yayi kamari.
Gwamnan ya gana da gwamnonin Arewa maso gabashin Najeriya.
Read Also:
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya zama wajibi Arewa ta tashi tsaye ta dauki matakin da ya dace kan yan bindigan da suka addabi mutane a gidajensu.
Zulum ya bayyana hakan ne a taron kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas karkashin jagoranicnsa. Wannan shine karo na uku da zasu hadu su tattauna, rahoton BBC Hausa.
Zulum ya ce dubi ga yadda matsalar rashin tsaro ta tabarbare a Arewa maso yamma irinsu Kano da Kaduna, akwai bukatar su tashi tsaye kada hakan ya shigo yankinsu.
Ya ce wajibi gwamnonin tabbatar da amince ga matafiyan a titunan da suka hada jihohin.