An Farmaki Sarki a Cikin Fadarsa a Jihar Ondo
Akoko, Ondo – Wani Sarki mai daraja ta daya a jihar Ondo, Owa na Ogbagi ya jikkata bayan kai masa hari har cikin fadarsa.
Basaraken mai suna Oba Victor Olasehinde Adetona, ya gamu da tsauysayin ne bayan wani mutum ya kai masa hari a fada.
Rahotanni daga Vanguard sun ce lamarin ya faru ne a yankin Akoko ta Arewa maso Yamma, inda wanda ake zargi mai suna Tope Adelani ya shiga fadar da misalin karfe 11:00 na safe.
An farmaki Sarki har cikin fadarsa
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa Adelani ya kai hari ga Sarkin, inda ya jikkata shi sosai kafin a garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa domin samun kulawa.
Majiyoyi sun ce wanda ake zargin ya kasance mai yawan zuwa fadar, kuma ya je wajen Sarkin domin neman aikin direba amma aka ce babu gurbi.
An ce bayan ganawar, Sarkin ya fita gonarsa, ya bar Adelani a fadar, amma rikici ya barke ne bayan dawowarsa daga gonar.
Read Also:
Rahotanni sun ce Adelani ya bi Sarkin zuwa cikin fada, ya kwace wayoyinsa tare da kashe su kafin daga bisani ya kai masa hari.
Yadda aka cafke matashi da ya farmaki Sarki
Iyalan Sarkin da suka yi kokarin shiga tsakani suma sun samu raunuka yayin da lamarin ya rikide zuwa fada mai tsanani.
Daga baya jami’an tsaron fada sun yi nasarar cafke wanda ake zargin tare da mika shi ga hukumomi bayan sun kwato wuka a hannunsa.
Matasan Ogbagi sun yi tir da harin, suna mai cewa abin ya sabawa al’adu da darajar mutanen yankin, tare da bayyana goyon bayansu ga Sarkin.
Sun kuma bukaci mazauna yankin su kwantar da hankula, su guji daukar doka a hannu, tare da kira ga gwamnati ta kara tsaro a fadar Sarkin.
Martanin yan sanda game da hari
Wakilin Legit Hausa ya tuntubi kakakin rundunar yan sanda a jihar, DSP Jimoh Abayomi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai Abayomi ya ce har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a kai korafin abin da ya faru da hukumarsu ta yan sanda ba sai dai ofishin NSCDC.






