A Cikin Watanni 8 Farashin Gas ya Karu da Kashe 100 a Najeriya

 

Gwamnatin Najeriya ta soma amfani da sabon harajin kashi 7.5 cikin 100 kan yadda ake sayar da gas din girki, yayin da farashinsa a yanzu ya karu da sama da kashi 100 a cikin watanni takwas.

Rahotanni na cewa gwamnati ta soma amfani da sabon haraji kan gas din da ake shigowa da shi kasar cikin mako uku da ya gabata, sannan an tilasta wa wasu diloli su biya haraji kan gas din da suka shigar da shi a watannin baya.

A yanzu tukunyar gas mai nauyin 12.5kg da ake sayarwa a kan 3,500 a Disambar 2020, a yanzu ana sayar da ita a kan 6,800 a wasu sassan Abuja.

Wasu mazauna Legas kuma na cewa suna sayen gas din a kan naira 7,200, kuma akwai hasashen zai iya kai wa naira 10,000 zuwa Disambar wannan shekara.

Wannan yanayi da ake ciki masana na cewa zai sake haifar da matsi musamman tsakanin marasa karfi da ke kukan tsadar rayuwa a kullum.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here