Ababen Fashewa: Mutane 20 Sun Mutu a Lebanon

 

M’aikatar lafiya a Lebanon ta ce aƙalla mutum 20 ne suka mutu a rana ta biyu da ƙarin ababen fashewa suka tashi a na’urorin sadarwar da mayaƙan Hezbollah ke amfani da su, sannan wasu 450 sun jikkata.

Hezbollah ta raba wa mambobinta na’urar sadarwa ta Pagers, saboda fargabar sojin Isra’ila za su iya musu kutse ta wayar salula tare da kashe mambobin ƙungiyar.

Yawancin fashewar ta faru ne lokacin da ake jana’izar waɗanda harin na ranar Talata ya shafa kusan mutum 12, inda dubu uku suka ji munanan raunuka.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here