Mutane Sunyi Asarar Dukiyoyinsu Sanadiyyar Fashewar Tankar Man Fetur a Jahar Adamawa

 

Wata babbar tankar dakon man fetur, ta yi hatsari a Yola, jahar Adamawa, inda lamarin ya haddasa gobara.

Rahotanni sun bayyana cewa tankar ta fashe ta kama da wuta, yayin da mutane suka yi asarar dukiyoyi masu ɗinbin yawa.

Wani mutumi da lamarin ya shafa ya bayyana cewa wutar ta cinye shaguna sama da guda 20.

Adamawa – Mutane sun yi asarar dukiya ta miliyoyin nairori da sanyin safiyar Litinin a wani lamarin gobara da ya auku a jahar Adamawa, kamar yadda Punch ta rawaito.

Lamarin ya faru ne yayin da wata tankar dakon man fetur, makare da man, ta kama da wuta bayan ta faɗi a shatale-talen Maidoki.

Rahotanni sun nuna cewa babbar motar dakon man fetur ɗin mai lambar rijista YLA 23 XM ta faɗi ƙasa ne yayin da take kokarin shan kwana a kan shatale-talen.

Shaguna da dama da kuma dukiyoyin mutane sun salwanta sun zama tamkar toka bayan motar da fashe kuma ta kama da wuta.

Babu wanda ya rasa rayuwarsa sanadiyyar wutar, amma mutane sun rasa dukiyoyin da suka kai kimanin miliyan N35m.

Ya mutane suka ji da lamarin?

Ɗaya daga waɗanda wutar ta yi wa ɓarna, kuma mamallaki wasu dukiyoyi da wutar ta cinye, ya bayyana cewa gobarar ta cinye shaguna sama da 20.

Yace:

“Motoci na guda biyu da kuma kayayyakin aikin mu na kasuwanci wutar ta lalata mana.”

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

A halin da ake cikin yanzun, jami’an hukumar kwana-kwana na jahar da kuma jami’an tsaro sun dira wurin domin kai ɗauki kan kiran da aka musu.

Hatsarin ya shafi jeka ka dawo da motoci ke yi a kan hanyar, yayin da direbobin motoci suka tattaru domin babu damar wucewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here