Faston da Yake da Hannu a Kisan Dalibar Lafiya ya Amsa Lafinsa
An kama wani fasto bayan ya amsa cewa yana da hannu a kisan wata daliba da ke karatun nas a tsakiyar Ghana.
Read Also:
Georgina Asor Botchwey, mai shekaru 22, ta bata ne a makon jiya kuma daga bisani an gano gawarta a wurin da aka binne ta.
An gano gawar Georgina ne a gidan wani hakimi da aka kira Nana Clarke a Mankessim, ta hanyar faston da aka kama.
Kazalika an gano jaka da takalmi da sauran kayayyakin matashiyar a gidan.
Yanzu haka jami’an tsaro na neman hakimin ruwa a jallo.