2023: Labarin Fastocin Kamfen Dina Ba Komai Bane Fa ce Kangon Kurege – Malami

Ministan shari’a, Malami, ya yi martani ga rahoton da ke ikirarin cewa fastocin kamfen dinsa na gwamna sun bayyana.

Ministan wanda yayi magana ta hadimin labaransa ya bayyana rahoton a matsayin karya tsantsa.

Sai dai kuma kakain Malami, Jibrilu-Gwandu, ya yarda cewa magoya bayan ministan a jahar na iya neman ya fito takara Ministan shari’a Abubakar Malami, ya karyata batun cewa fastocin kanfen dinsa na gwamna sun karade unguwanni a jahar Kebbi.

A cewar jaridar Premium Times, hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Umar Jibrilu-Gwandu a Birnin Kebbi a ranar Juma’a.

Mista Jibrilu-Gwandu na martani ne ga wani rahoton kafofin watsa labarai da ke nuna cewa fastocin kamfen din ministan na 2023 sun karade unguwanni a fadin jahar.

“An janyo hankalinmu zuwa ga wani rahoton karya da ke ikirarin cewa fastocin Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a na neman kujerar gwamna a zaben 2023 sun cika ko ina a jahar.

“Mun karade birnin tare da yan jarida, sun gani da idanunsu cewa babu kamshin gaskiya a rahoton. Bamu ga kowani fosta makamancin haka ba a Birnin Kebbi.

“Don haka, muna so jama’a su yi watsi da wannan labari saboda hasashen mawallafin ne kawai,” in ji shi.

Mista Jibrilu-Gwandu ya bayyana cewa ministan na da magoya baya da dama a jahar da ka iya nuna ra’ayi a kansa, saboda taimakon al’umma da alkhairinsa, inda ya kara da cewa labarin fastocin kamfen dinsa ba komai bane face kangon kurege.

“A yanayi da wani zai shirya karairayi da sunan aikin jarida yana bata sunan aikin ne.

“Idan kun tuna, a ranar 16 ga watan Maris, 2020, Malami ya bukaci magoya bayansa da su janye daga batun kamfen din neman takarar gwamnansa na 2023, domin lokaci bai yi ba na kamfen din siyasa kamar yadda yake a dokar zabe na kasa,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here