Fara Jigilar Man fetur ɗin Dangote Zai Rage Farashin Sufuri da Abinci – CBN

 

 

Babban Bankin Najeriya CBN ya ce fara jigilar man fetur daga matatar man fetur ta Dangote zai rage farashin sufuri da abinci.

Mista Olayemi Cardoso ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai a ranar Talata, bayan taron kwamitin tsare-tsaren harkokin kuɗi wato MPC a Abuja.

“Kwamitin ya nuna ƙwarin gwiwar cewa samar da man fetur daga matatar man fetur ta Dangote zai taimaka wajen rage farashin kayan masarufi.

“Haka kuma zai taimaka wajen rage buƙatun kuɗaɗen ƙasashen waje da ake yi domin shigo da man fetur Najeriya,” in ji Cardoso.

A watan Satumba ne babban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, ya fara jigilar man fetur karon farko daga matatar man Dangote, kamar yadda tashar talbijin ta Channels ta ruwaito.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here