FG ta yi Magana Akan Wada Aka Yankewa Hukunci a UAE
FG ta magantu a kan ma su daukan nauyin Boko Haram da aka yankewa hukunci a UAE.
Ta ce suna iya daukaka kara zuwa kotun kolin Daular Larabawar idan suka yi muradi.
Abike Dabiri-Erewa ta bukaci yan Najeriya a fadin duniya da su guji aikata laifi a duk inda suke Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yan Najeriya shida da aka yanke wa hukuncin ta’addanci a kasar hadaddiyar Daular Larabawa na iya daukaka kara a kotun koli ta UAE.
Gwamnatin ta bayyana cewa masu laifin sun sha kaye a karar da suka daukaka amma cewa suna iya sake daukaka kara a gaban babbar kotu a Daular idan suka so.
Mutanen da aka yanke wa hukunci a kan daukar nauyin Boko Haram ana zarginsu da tura zunzurutun kuɗaɗe har Dala $782,000 ga yan ta’addan.
Read Also:
Sai dai rahoton Daily Trust ya nuna cewa yan uwansu sun yi ikirarin cewa makirci aka kullawa mazan. Rahoton ya kuma bayyana cewa biyu daga cikin waɗanda ake zargin, Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf an yanke musu hukuncin zaman gidan yari iya tsawon rayuwarsu.
Sauran mutane huɗun da suka haɗa da; Ibrahim Ali Alhassan, AbdurRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf, da Muhammad Ibrahim Isa, dukkansu an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara goma.
Amma da take martani a kan lamarin, shugabar hukumar da ke kula da yan Najeriya a kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta ce mazajen na iya tunkarar kotun koli ta UAE “idan suka yi muradin haka.”
Dabiri-Erewa a wani wallafa da tayi a shafin Twitter a ranar Litinin, ta ce: “Suna iya tunkarar kotun koli idan suka yi muradin haka yayinda muke ci gaba da kira ga dukkanin yan Najeriya a duniya da su guji laifi da ta’addanci. Lamarin na a kotu tun 2015.”
Kakakin ma’aikatar harkokin waje, Mista Ferdinand Nwonye, ya ce gwamnati za ta bi hanyoyin da take dashi harda na diflomasiyya wajen taimakawa masu laifi. Amma ya bayyana cewa babu wani jawabi a hukumance kan lamarin a yanzu