LABARINA SERIES: Dalilin Ficewar Sumayya Daga Shirin – Dr.SYS

Abinda ya faru,
Dalilin ficewar Nafisa Abdullahi (Sumayya) daga series din.
Wace zata maye gurbin ta?

Daga Sameen Y Saeed (Dr.SYS)

Labarina series, shine daya tilo tun kafuwar masana’antar shirya fina-finai ta “Kannywood”, ba’a taba wani “series film” da’ake kallonsa kuma yasamu karbuwa da comments iri-iri na mutane. Wannan yafaru ne saboda tsarin yadda labarin ya tsaru dakuma irin gogewa wajen fitar da “emotions” na abubuwan dake faruwa aciki. Dukda cewa Labarine ajiyayye kusan shekara 2, sannan aka fara haska shi.

Labarina series, yasamu wannan nasarori ne ta hanyar manyan dalilai uku (3)sune kamar haka; (1) Marubuci (Scriptwriter), (2) Ma’akaita (Crew) dakuma (3) jarumai (Actors/Actress).

(1)- Marubucin Labarina (a karon farko wato season 1,2,3) shine; Ibrahim birniwa. wanda gogagge ne wajen iya rubutun film sama da shekara 15.
Sedai bayan wasu dalilai daga baya aka canja marubucin, wani marubucin kuma ya dauki ragamar cigaba da rubutawa (ko ince marubuta).

(2)-Ma’aikata (Crew) sunada matukar mahimmanci wajen samar da shirin film kowanne iri; wanda sune suke samar da “90 percent” na kasancewar film. Anan zamu dauki me bada umarni (Director) saboda duk wani aiki yana karkashin ikon sa, wanda shine Aminu Saira. Kowa yasan Saira wajen gogewa a harkar bada umarni.

(3)- Jarumai (Actors/Actresses): cikin 10% na kammalar film yana karkashin rikunin jarumai, jarumai sune masu taka rawa iri-iri cikin shirin, kuma su akafi kallo a kowanne bangare; ma’ana shi me kallon film babu ruwansa da marubucin da kuma crew ko ma’aikata. Don haka jarumai sune film (a wajen me kallo).

Meye dalilin ficewar Nafisa Abdullahi?
Kamar yadda rahotanni ke xuwa cewa jarumar ta nuna rashin sha’awarta da cigaba da jan ragamar shirin a wata wasika da ta aikawa kamfanin “Saira movies” dauke da saka hannunta, da kuma nuna aiki ne yayi mata yawa bazata iya cigaba da futowa acikin shirin ba.

To a fahimta ta wannan yanada alaqa da lalacewar da shirin yayi tun farkon season 4, kasancewar canja marubucin; abune sananne awajen marubutan film (Screenwriter) da kuma masu tsara labari (Screenplayers) duk sanda aka canja marubuci da wahala labari ya dore! Saboda za’a rasa “plotline” ko “storyline” na ainashin farkon labarin; dukda cewa wadanda suka cigaba da rubutun “experts” ne a harkar rubutu, daga cikinsu akwai Nasir S. Gwangwazo, Editor na jaridar blueprint Hausa, dakuma yakubu m. Kumo.

Idan mun fahimta, tun farkon season 4 aka dauke manyan jaruman da film din yafara ginuwa akansu, wato “leading-characters” ko “villains” ma’ana andauke Mahmood (Nuhu Abdullahi), annuna ya mutu. Haka ita kuma Sumayya (Nafisa Abdullahi) an nuna anyi “kidnapping” dinta. Mutane suna ganin shirin yafara sauka daga yadda aka dauko shi a farko!

Wannan dalilin zai iya sakawa ita jaruma “Sumayya” taji bata da ra’ayin cigaba da taka rawa acikin shirin, tunda alamu sun nuna zasu iya tafiya ba tare da ita ba.

Kokuma dalili na biyu, ita jarumar (Sumayya) tagaji da shirin, saboda yana iya shigar mata “schedule” dinta nadaban. Dama kowane jarumi ko jaruma bukatarsa film yayi tasiri akansa yasa shi suna ~ to dama ita Nafisa Abdullahi tayi suna tun kafin Shirin Labarina.

A karshe, da akwai yuwuwar wasu jaruman za’a canja su ko Kokuma labarin yabatar dasu a ‘next season’ wato “season 5″, haka kuma za’a kawo wasu, sedai har yanxu ana ta tunanin wace zata cigaba daga inda Nafisa Abdullahi ta tsaya a ‘role’ dn Sumayya.

Wasu suna tunanin jaruma ”Fati washa” zata dauki ragamar, wasu suna hangen “Aisha humaira” wasu kuma suna tunanin wata ce daban, amman inaga bawai fuska, kwalliya Kokuma wani abu daban ‘role’ din Sumayya ke bukata ba sedai “Emotion”, saboda haka duk wacce za’a saka yazamana zata iya futar da wannan emotions da ‘role’ din yake bukata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here