FIFA ta Dakatar da Shugaban ƙwallon ƙafar Sifaniya,Luis Rubiales

 

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya Fifa ta dakatar da Luis Rubiales daga matsayinsa na shugaban hukumar ƙwalon ƙafar Sifaniya kan sumbatar ‘yar wasan ƙwallon ƙafar ƙasar.

Fifa ta dakatar da da Mista Rubiales daga shiga harkokin ƙwallon ƙafar a ƙasar da ma matakin duniya baki ɗaya.

Sumbatar Jenni Hermoso da Rubiales ya yi a leɓenta bayan da Sifaniya ta doke Ingila a wasan ƙarshe na Kofin Duniya ya janyo ce-ce-ku-ce mai zafi a duniyar wasannin.

Inda aka riƙa kiraye-kirayen ya sauka daga muƙaminsa sakamakon sumbatar Hermoso.

To sai dai ya ƙi yin murabus yana mai cewa ya aikata hakan ne a cikin murna, dan haka bai ɗauke shi a matsayin wani abu ba.

A ranar Alhamis ne Fifa ta buɗe bincike a hukumance kan Mista Rubiales mai shekarar 46.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com