Gwamnatin Jahar Filato ta Dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na Jahar

 

Gwamnan jahar Filato ya tabbatar da dakatar da shugaban jam’iyyar APC na jahar bayan makwanni.

An dakatar da shugaban ne bisa zargin yiwa jam’iyyar APC zagon kasa, lamarin da bai yi wa jam’iyyar dadi ba.

Tuni gwamnan jahar ya sanar da nadin sabon shugaban jam’iyyar jiya Asabar a yayin taron ranar dimokradiyya.

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya tabbatar da tsige Cif Letep Dabang a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jahar, Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a daren Asabar yayin wata liyafar cin abincin dare da aka shirya ta masu ruwa da tsaki a matsayin wani bangare na ayyukan bikin ranar Dimokiradiyya ta 12 ga Yuni wanda aka gudanar a gidan Gwamnatin Rayfield da ke Jos.

Lalong a jawabinsa ya gabatar da sabon Shugaban Jam’iyyar APC na Jahar in da yake cewa:

“Muna da sabon shugaban jam’iyyar APC a Filato. Yana nan tare da mu. Na gan shi yana kokarin aika sakon tes ta hanyar amfani da wayarsa na ce, bari na tsaya a nan na gabatar dashi kafin ya bace mani.”

Duk da cewa Gwamnan bai kara magana a kan lamarin ba, amma an tattaro cewa ana zargin tsohon shugaban wanda Mataimakinsa, Enough Fanmak ya maye gurbinsa, da aikata zagon kasa ga jam’iyyar lamarin da ya sa aka dakatar da shi.

Dakatar da Dabang na kunshe ne a cikin wata wasika da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sanata John Akpanudoedehe ya rubuta masa. Wasikar mai dauke da kwanan wata 11 ga Yuni, 2021, ta ce,:

“Jam’iyyar na takardar da ta dakatar da kai daga ofis a matsayin Shugaban riko na Jaha na reshen Filato na jam’iyyarmu, kan yiwa jam’iyya zagon kasa.”

Gwamnan ya yi tir da amfani da kafafen sada zumunta wajen yin barazana ga Najeriya

Har ila yau, an ruwaito cewa, Gwamna Simon Lalong ya yi tir da yadda ake amfani da kafofin sada zumunta wajen yin barazana ga dimokradiyyar Najeriya.

Ya ce wasu ‘yan Najeriya suna amfani da kafafen sada zumunta wajen yada manufofinsu na kashin kansu ba tare da lura ga kiyaye mutuncin dimokiradiyyar Najeriya ba.

Lalong ya ce “Wani lokacin, idan ka bi abin da wasu mutane suka sanya a kafofin sada zumunta, za ka yi tunanin anya ko sun yi imani da Najeriya?”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here